1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na shirin fafatawa da 'yan aware

Mouhamadou AwalNovember 8, 2014

Sojojin Ukraine na shirin afkawa 'yan awraen gabahin ƙasar da yaƙi.

https://p.dw.com/p/1DjIx
Ukraine Gefechte 5.11.2014
Hoto: picture-alliance/dpa/Alexey Kudenko

Shugaban Petro Poroschenko na Ukriane ya yi tir da matakin da Rasha ta ɗauka na turo da tankokin yaƙi da kuma manyan makamai a kan iyaka Lughansk da ke gabashin ƙasar. Rundunar sojojin wannan ƙasa ta nunar da cewar motoci yaƙi 32 da kuma makamai atilari ne Rashar ta aika wa 'yan aware domin su ci gaba da tada zauna taye a Ukraine.

Idan za a iya tunawa dai, ɗaruruwan mutane ne dai suka rigamu gidan gaskiyya tun byan ɓarkewar rikici tsakanin dakarun gwamnatin Ukraine da kuma masu goyon bayan Rasha a wannan yanki. Wakiliyar DW a Ukraine ta ce wannan takun saka na ci gaba da hauhawa ne sakamakon shirin da sojojin gwamnati ke yi na afkawa 'yan aware da ke goyoyn bayan Rasha.

"Wannan dai shi ne shingen ƙarshen da sojojin Ukraine ke gudanar da bincike a cikinsa a kan hanyar da ta haɗa Mariopol da kuma Donetsk da ke hannun 'yan aware. hankulan sojojin dai na tashe,ko da shi ke dai sun sha alwashin ci gaba da dagewa a kan matsayinsu."