Uganda ta hana musabaha dan takaita yaduwar cutar Marburg | Labarai | DW | 08.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Uganda ta hana musabaha dan takaita yaduwar cutar Marburg

Wannan ne karo na biyu da cutar Marburg mai alamu masu kama da ta Ebola ke barkewa a kasar Uganda, yanzu haka mutun guda ne ya hallaka a dalilin wannan cuta.

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya yi kira da al'ummarsu da su daina masabaha da juna, a daidai wannan lokacin da kasar ke kokarin yaki da wwata kwayar cuta mai suna Marburg wadda ke da alamu irin na Ebola.

Kawo yanzu dai mutun guda ne ya rasu a yayinda wasu uku kuma suke kebe dan tantance ko suna dauke da cutar, bayan da mutun gudan ya mutu ranar talata inda ranar lahadi ne aka sanar da bullar wannan cuta. Wadannan mutane ukun suna kebe ne a wani wurin kulawa da ke Entebbe daka wajen babban birnin kasar wato Kampala kuma daya daga cikinsu yaro ne dan shekaru bakwai (7) da haihuwa.

Ita ma wannan kwayar cutar tana da hadarin gaske kuma kamar Ebola, ita ma ana yada ta ne ta ruwan da ke fita daga jikin dan adam, sannan ta kan dauki kwanaki 21 kafin ta kenkeshe ta fara tasiri a jikin mutun. A shekarar 2012 ma wannan cuta ta barke a kasar Uganda inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 10.