Fafaraoma Francis zai kai ziyara Daular Larabawa
February 3, 2019Talla
Rahotannin na nuni da cewa ya karbi goyon gayyata ne daga yerima mai jiran gado na kasar Sheikh Mohammed Bin Zayed al-Nahyan. Gabanin ziyarar, shugaban cocin katolikan ya baiyana damuwa kan yakin kasar Yemen na fiye da shekaru hudu, inda ya shawarci bangarorin da ke rikici da juna da su amince da yarjejeniyar zaman lafiya domin bayar da daman shigar da agaji ga mabukata da rikicin ya kassara.
Francis ya kasance Fafaroma na farko da ke irin wannan ziyara a yankin kasashen Larabawa a tarihi.