1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Twitter zai kafa reshe a Afirka

April 12, 2021

A karon farko, kamfanin Twitter, ya ce zai dauki ma'aikata a nahiyar Afirka inda ya shirya bude cibiyarsa a Ghana nan gaba kadan. Kamfanin ya ce zai dauki ma'aikata.

https://p.dw.com/p/3rtpd
Twitter Logo
Hoto: Imago Images/Zuma/O. Marques

Kamfanin na Twitter, ya bi sahun takwaransa a bangaren sada zumunta na zamani Facebook da ma karin wasu 11 wajen shiga kasashe nahiyar ta Afirka.

A wata ziyarar da ya kai kasashen Najeriya da Ghana da Ethiopia da ma Afirka ta Kudu a bara, shugaban Twitter, Jack Dorsey, ya ce Afirkar za ta kasance a kan gaba wajen tsara makomar ci gaban wannan duniya.

Tuni ma dai aka tallata wasu manyan mukamai 11 da za a dauki ma'aikata a Ghana, a fannonin da suka hada da kwarraun injiniyoyi da na kasuwanci da ma wadanda suka kware a harkar sadarwa.