Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Wannan shirin DW mai suna "Tushen Afirka" na amfani da majigi da rahotannin rediyo wajen bayyana siffofin mashahuren mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka.
Ficen da masarautar Dahomey, tsakanin karni na 17-19, da a yau ake kira Jamhuriyar Benin, ya samu ne saboda kafa wata rundunar mayaka da ta kunshi mata zalla, wadanda aka kira ''Dahomey Amazon''.
Ana daukar Taytu Betul a matsayin daya daga cikin shahararrun shugabannin Habasha, mata ce ga sarkin sarakuna Menelik II. Ta taka rawa wajen murkushe 'yan mulkin mallaka na Italiya ita ce kuma ta kafa birnin Addis Ababa.
Ya kasance babban hafsan hafsoshin soji da ya taimaka wa Sarki Menelik II na Habasha karfafa iko kan yankunan kudu. Amma ayyukan da Gobena Dache ya gudanar na fama da cece-kuce.
Sarki Rudolf Douala Manga Bell da yai karatunsa a Jamus, yana son al'adar Jamusawa. Sai dai daga baya Turawan mukin mallaka na Jamus sun ba shi kunya, lokacin da suka sauya akalar al'ummar kasarsa.
Abla Pokou sarauniya ce ta Akan wadda ta jagoranci jama'arta daga kasar Ghana ta yanzu zuwa Ivory Coast a 1770, tarihi ya nuna ta sadaukar da danta ga iskoki domin mutanenta su ketara kogi.
Sarkin daular Mali Kanku Musa ya kasance mutum mafi karfin arziki da aka taba samu a duniya. Wadatarsa ta ba shi damar maida Timbuktu cikin birni mai ban mamaki. Ya yi sarauta tsakanin shekarar 1313 zuwa 1337.
Gimbiya Yennenga ta kasance jaruma a fagen yaki kuma kwararriya wajen hawa doki. Ta bar tarihi mai dorewa a Burkina Faso.
An haife ta a Birtaniya da duk dama da take da ita amma Helen Joseph ta yi kasadar kalubalantar mulkin nuna wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. DW ta tattauna rayuwarta da dan gwagwarmaya Carl Niehaus.
Shawarar ba wa mai rajin kare muhalli kyautar zaman lafiya ta Nobel ta zo da mamaki a 2004. Sai dai ta jaddada rawar da kungiyar Green Belt ta Wangari Maathai ta taka wajen gina wata al'umma mai son zaman lafiya.
Dedan Kimathi ya jagoranci gwagwarmayar Mau Mau, kungiyar da ta sama wa Kenya 'yanci da karfin yaki. Ana ganin shi ne ya jagoranci juyin juya hali da ya kawo karshen mulkin mallakar turawa kafin a kashe shi a karshe.
Sarki Afonso I na Kwngo, ya kulla alakar cikin hikima da kasar Portugal da wata manufa ta samun riba. Da fari ya kulla cinikin bayi a tsakaninsu amma abin ya dagule daga bisani.
A shekara ta 1839, an saci Sengbe Pieh, wani manomi kuma dan tireda daga Saliyo a matsayin bawa. Kan hanyar zuwa Amirka ya jagoranci tawaye a cikin jirgin ruwan jigilarsu, abin da ya kawo karshen cinikin bayi a Amirka.
Léopold Sédar Senghor, wanda ake yi wa kallon dattijo a Afirka, masani ne kuma marubucin wakoki. Bayan zama gidan yari lokacin yakin duniya, ya kasance shugaban kasar Senegal na farko
Da ilimin zamani kalilan karkashin gwamnatin nuna wariyar launin fata, Hamilton Naki ya tashi da mai kula da furenni zuwa babban mai kula da dakin bincike da ake girmamawa.
Eduardo Mondlane yana da hangen 'yanci da hadin kan Mozambik, daga Turawan mulkin mallaka na Potugal. Ko da yake an halaka shi yayin da yake gudun hijira a ketere, amma an ci gaba da manufofinsa.
'Yar Najeriya mawallafiya Flora Nwapa, littafinta Efuru ya sa ta zama mace ta farko da ta wallafa littafi da turanci. Aikinta ya share fage ga baiyanar mata mawallafa a Najeriya da sauran kasashen Afirka.
Fiye da karni biyar bayan sarautarsa, gadon da Oba Ewuare ya bari na nan daram a cikin garin Benin. Ana tunawa da karfin ikonsa da kuma habaka fasahar sarrafa tagulla da ake cin amfani har yanzu.
Sunan Shaka Zulu na da nasaba da yaki. Dakarunsa kan tarwatsa duk wanda ya sha masa gaba. DW ta yi hira da masanin tarihi Maxwell Shamase wanda yake ganin an gurbata tarihin Shaka.
A lokacin da maza suka mamaye harkokin rayuwa, aka samu Sarauniya Amina ta Zazzau. Gwarzuwa Bahaushiya, wadda ta jagoranci yaki domin fadada daula.
Laberiya kasa ce ta 'yantattun bayi, wadda aka gina da musguna wa 'yan kasar lokacin da aka zabi William Tubman a matsayin shugaban kasa. Bayan hada kan mutane, ya shirya kasar bisa tsarin ci-gaba wanda bai samu ba.
Lokacin da Tanzaniya ta samu 'yanci Julius Nyerere ake dauka a matsayin uban kasa. Amma da ba domin Bibi Titi Mohamed, da ya rasa jigo wajen samun wannan nasarar.
Ya kasance malamin addini da ya jagoranci juyin-juya hali: Usman dan Fodio da ake wa al'kunya ta ladabi da Shehu, ya yi suka ga sarakuna tare da kawo sauyi a tsarin siyasa a yankin da yanzu ya kasance arewacin Najeriya.
Nelson Mandela ya fito daga kurkuku bayan shekaru 27 don kwatar 'yanci daga fararen fata da ke mulki a Afirka ta Kudu. Ya zama bakar fata na farko shugaban Afirka ta Kudu kuma ya samu lambar Nobel.
Kwame Nkrumah shi ne shugaban kasar Ghana na farko, bayan jagorantar kasar wajen samun 'yancin kai. Ya samu gogewa a matsayin malamin makaranta a kasashen Amirka da Ingila.
An haifi Cheikh Anta Diop a shekarar 1923 a kauyen Thieytou da ke da tazarar kilomita 100 gabas da birnin Dakar na kasar Senegal. Danginsa 'yan kabilar nan ce ta Wolof.
Duk da sauyi daga 'yar aikatau zuwa mai jan hankali na ban mamaki Sarah Baartman, a Turai ana mata kallon gwagwgwon biri.
Sarkin babbar daula Haile Selassie, zakin Judah wanda ya gaji sarauta mai tsawon tarihi na shekaru aru-aru. Ya samar da sauyi na ci-gaba sabanin tunaninsa. Sauyin ya zama silar raba shi da gadon sarautarsa.
An santa a matsayin "uwar masu fafutukar 'yancin bakar fata a Afirka ta Kudu" Charlotte Mannya Maxeke an boye tarihinta da gudunmawar da ta bayar a harkokin da suka shafi ilimin yara da matasa a Afirka ta Kudu.
Yana daga cikin wadanda ba a sani sosai ba, da suka taka rawar samun 'yanci a kasashen Afirka, amma Yarima Louis Rwagasore ya jagoranci Burundi cikin kwanciyar hankali bisa hanyar samun 'yanci.
Nyerere wanda fitaccen dan kishin kasa ne ya taimaka wajen ganin Tanganyika ta samu mulkin kai, inda daga bisani ta hade da Zanzibar a matsayin kasa guda da ake kira Tanzaniya.
Da sake hada Daular Afirka ta Yamma wacce ta kasance a rarrabe a karni na 13, Soundiata Keita ya kafa daular da har yau ta yi suna. Soundiata Keita ya kasance jarimi kana jagoran al'umma.
Margaret Ekpo mace jajirtacciya mai bayyana ra'ayinta, ta bude idanun mata sun fito an fafata da su a fagen kare hakkinsu da shiga siyasa. Ta taimaka wajen sauya siyasar Najeriya a lokacin da maza suka mamaye al’amura.
Kwarangwal Lucy wacce aka fi sani da suna Dinknesh tana da shekaru miliyan 3.5. Kuma kasusuwa ne na bil Adama. An ganota a shekara ta 1974 a kasar Habasha.
A fafutukarsa ta kishin kasa, Amílcar Cabral ya jagoranci Gini Bissau da Cape Verde wajen samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, amma an hallaka shi kafin hakarsa ta cimma ruwa.
Masana tarihi na tababa game da gaskiyar tarihin Bayajidda amma mutumin wanda ake dauka a matsayin gwarzo na ci gaba da kasancewa a tarihin Malam Bahaushe.
Yaa Nana Asantewaa ta yi fice a kan rawar da ta taka a fage na jarumta a yakin kujerar gwal wato Golden Stool. Mace ce mai jajircewa. A baki dayan rayuwarta ta yi kokari wajen kare daularta.
Daga ma'aikacin aike sakonni zuwa firaminista a cikin shekaru kalilan: Patrice Lumumba ya saka karfinsa cikin yaki da Turawa 'yan mulkin mallaka a gaban duk wani kalubale.
Ahmed Baba ya kasance daya daga cikin manyan malamai na Afirka a karni na 16. Marubuci kana masanin addinin Islama, ya yi aiki game da shari‘a kan batun bauta da rubuta tarihin mashahuren mutane.
Josina Machel ta yi kokari a fafutukar kare hakkin mata karkashin Turawan mulkin mallaka. Sai dai ta mutu tana da shekaru 25 ba tare da ganin cikar burinta na samun 'yanci a kan idonta ba.