Tururuwar neman mujallar Charlie Hebdo | Siyasa | DW | 14.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tururuwar neman mujallar Charlie Hebdo

Duk da harin ta'addancin da aka kan ofishin buga mujallar barkwancin nan ta Charlie Hebdo makon jiya a birnin Paris, sabuwar mujallar kamfanin ta sake fitowa.

Duk da harin ta'addancin da aka kan ofishin buga mujallar barkwancin nan ta Charlie Hebdo makon jiya a birnin Paris, sabuwar mujallar kamfanin ta sake fitowa, inda aka buga sama da miliyan biyar maimakon dubu 30 da ta saba sayarwa cikin mako. Hakan dai na zuwa ne bayan da shugabannin addini da na siyasa a Jamus sun gudanar da wani gangamin adawa da ayyukan ta'addanci tare da nuna alhini ga wadanda hare-haren na birnin Paris ya ritsa da su.

Dubun dubatan mutane ne suka yi dogon layi a gaban shaguna sayar da jaridu a fadin duniya don sayen sabuwar mujallar kamfanin na Charlie Hebdo, wanda a ciki ta sake yin zanen wani mutum da ta ce Annabi Mohammad ne SAW. Duk karin yawan mujallun kimanin miliyan biyar da kamfanin ya buga, to amma duk an saye. Kuma mutane na ci gaba da yawon nema.

Kamfanin na Charlie Hebdo da ya saba buga mujallar kimanin dubu 60 a mako kuma da kyar yake iya sayar da rabinsu, a wannan mako ya buga miliyan biyar kuma ya ce zai kara yawansu idan bukatar haka ta ta so.

Mutane 17 suka rasu a harin da wasu 'yan ta'adda 'yan uwa juna biyu suka kai kan kamfanin a makon da ya gabata da kuma wanda wani dan bindiga ya kai kan wani kantin Yahudawa da ke birnin Paris. Don ganin wannan lamarin bai kai haddasa gaba tsakanin al'umma mabiya addinai da al'adu daban-daban ba, a ranar Talata shugabannin siyasar Jamus da suka hada da shugabar gwamnati Angela Merkel da shugaban kasa Joachim Gauck sun halarci wani taron gangamin adawa da ayyukan ta'addanci da kuma kyamar baki da kungiyoyin Musulmin kasar suka kira a birnin Berlin.

A jawabinsa ga taron shugaban Jamus Joachim Gauck cewa ya yi ba za mu mika wuya ga 'yan ta'adda ba.

Gangamin dai na zama wata manuniya ga masu son cusa gaba tsakanin al'umma da ke zama cikin kwanciyar hankali da lumana da juna.

Daga can kasashen Larabawa irinsu Masar ma an yaba da wannan gangamin da kungiyoyin addinin Musulunci a Jamus suka shirya a birnin na Berlin, musamman bayan harin na Paris da kuma bullar masu adawa da yaduwar addinin Musulunci a Jamus, yanayin da ke sanya fargaba zukatan baki a cikin kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin