Turkiyya: Za mu saki Bajamushen | Labarai | DW | 14.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya: Za mu saki Bajamushen

Gwamnatin kasar Turkiyya ta ce akwai yiwuwar ta saki dan jaridan nan haifaffen kasar Jamus wanda ta tsare ba tare da wani tuhuma ba tsawon shekara guda.

Firaministan kasar Turkiyya Binali Yildirim ya bayyana fatar sakin dan jaridan nan haifaffen kasar Jamus wato Deniz Yücel bayan zaman shekara guda a gidan yari a Turkiyyar. Cikin wata hirar da ya yi da kafar yada labarai na gwamnatin Jamus ARD, Binali Yildrim ya tsaya kan cewar kotunan kasar Turkiyya, kotuna ne da ke aiki ba tare da wani amshin shata ba.

Kama dan jaridan da wasu Jamusawa a Turkiyya dai, ya kara dagula kokarin kyautata dangantaka tsakanin gwamnatin Angela Merkel da ta shugaba Erdogan na Turkiyya.

Ana dai tsare da Yücel ne ba tare  da tuhumarsa da laifinba a gaban kotu. Denis Yücel dan shekaru 44 wanda aka haifa a kusa da Frankfurt wanda mahaifinsa baturke ne wanda ke yi wa jaridar Die Welt aiki an kamashi tun a cikin watan Maris na shekara ta 2017.