Turkiyya : ′Yan adawa sun yi watsi da samakon zabe | Labarai | DW | 20.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya : 'Yan adawa sun yi watsi da samakon zabe

Yayin da hukumar zaben Turkiyya ke tabbatar da amincinta kan zaben kasar na ranar Lahadi, jam'iyyun adawa sun lashi takobin kai batun babbar kotu don a bi musu kadi.

Hukumar zaben kasar ta Turkiyya ta yi watsi da kiraye-kirayen jam'iyyun adawar kasar na a soke zaben raba gardamar fadada karfin ikon shugaban Raccep Tayyip Erdogan da aka yi a farkon wannan makon, zaben da aka yi zargin kura-kurai a cikinsa.Hakan dai ya haddasa zanga-zanga daga 'yan kasar wadanda suka yi kiran da a rusa majalisar jagororin hukumar zaben kasar, yayin da a daya hannun masu adawar ke tabbatar da cewar za su kai batun gaban babbar kotun kasar.