Turkiyya ta karyata zargin ganawa ′dan jarida azaba | Labarai | DW | 12.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya ta karyata zargin ganawa 'dan jarida azaba

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta karyata korafin Deniz Yucel 'dan jarida mai nasaba da kasar Jamus, cewar jami'an tsaron Turkiyya sun gana masa azaba.

Ma'aikatar ta kuma yi watsi da gargadin da takwararta ta tarayyar Jamus tayi kan ta kiyayi karya ka'idojin da Majalisar Dinkin Duniya ta tanadar kan yaki da ganawa mutane azaba, bayan ta zargi Jamus ta rashin hujjojin da zasu tabbatar jami'an tsaro a Istanbul sun aikata abinda ake zarginsu da shi cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Turkiyya Hami Aksoy ya rabawa manema labarai.

A makon daya gabata ne Yucel wakilin jaridar Die Welt mallakar kasar Jamus, ya bayyana yadda jami'an tsaron suke lakada masa duka bayan kaskanci da kuma barazanar da ya dinga fuskanta,  a lokacin zamansa a gidan yarin Silivri dake Santanbul. Turkiyya dai ta zargi 'dan jaridar ne da laifin alaka da mambobin jam'iyyar PKK ta Kurdawa da kuma wasu almajiran Malamin addinin Islaman nan Fethullah Gulen wanda gwamnatin Turkiyya ke zargi da shirya juyin mulkin da baiyi nasar ba tun a shekara ta 2016.