Turkiyya ta kai sabbin hare-hare a Idlib | Labarai | DW | 02.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya ta kai sabbin hare-hare a Idlib

Wasu hare-hare da Turkiyya ta kaddamar a Siriya, sun hallaka dakarun Shugaba Bashar al-Assad akalla 19 daidai lokacin da kasashen ke ci gaba da nuna wa juna yatsa.

Wani jirgin sama marar matuki ne dai ya kai harin kan jerin gwanon motocin sojin na Siriya a yankin Jabal al-Zawiya, kamar yadda kungiyar da ke sa ido kan yakin wato Syrian Observatory for Human Rights, mai cibiya a Birtaniya ta tabbatar.

Labarin ya kuma zo ne sa'o'i kalilan bayan kakkabo wasu jiragen yakin Siriya da Turkiyyar ta yi a yankin Idlib da ke arewacin Siriya.

Wannan dai yanki ne da Turkiyya ke goyon bayan mayakan da ke yi wa gwamnatin Siriya tawaye da ma kokarin kwace iko daga hannunta.

A makon jiya ne mayakan Siriya suka hallaka dakarun Turkiyya 34, abin da ya janyo martani daga Turkiyyar.