Turkiyya ta gargadi mutanenta kan zuwa Turai | Labarai | DW | 29.01.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya ta gargadi mutanenta kan zuwa Turai

Ma'aikatar kula da harkokin wajen kasar ta ce wannan mataki ya zama wajibi ganin yadda masu tsattsauran ra'ayi ke adawa da addinin Islama da manufofin kasar ta Turkiyya a kasashe dabam-dabam na nahiyar Turai.

Turkiyya ta gargadi 'yan kasarta da su dakatar da tafiye-tafiye zuwa kasashen nahiyar Turai, idan har ba su zama dole ba.Turkiyyar ta ce batancin da ake yi wa  Qur'ani mai tsarki, na nuna tsangwamar al'adun ketare da Turawa ke yi.

Gargadin na Turkiyya na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da kasashen Denmark da Finland da Norway da Sweden, inda Turkiyya ta ce an wulakanta littafi mai tsarki, suka bukaci mutanen kasashensu da su kaurace wa yin balaguro zuwa Turkiyya.