Turkiyya: Soma shiri′ar wadanda ake zagi da juyin mulki | Labarai | DW | 01.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya: Soma shiri'ar wadanda ake zagi da juyin mulki

An soma babban zaman shari'a da ya shafi mutane kusan 500 da ake zargi da hannu a juyin mulkin da bai yi nasara ba na bara na watan Yulin bara a Turkiyya.

Turkei Ankara - Angeklate werden zu Gericht gebracht (picture-alliance/abaca/Mustafa K.)

Sojoji sun kawo wadanda ake zargi da laifin yunkurin juyinn mulki a gaban kotu a Turkiya.

Shari'ar na gudana ne a wani zaure na musamman da aka tanada a gidan kaso na Sincan da ke daf da Ankara babban birnin kasar ta Turkiya inda ake tsare da mutanen. An soma shari'ar ne da wajejen karfe 10 agogon kasar ta Turkiyya a babban zauran da ka iya daukan mutane fiye da 1500, wanda aka gina musamman ma sabili da shirya wannan shari'a.

Sai dai an samu mutane da dama dauke da kwalaye a harabar kotun da ke kiran a yankewa wadanda ake zargin hukuncin kisa, tare da furta kalamai na kyama a gare su. Hukumomin kasar ta Turkiyya dai sun ce tun daga sansanin sojojin saman kasar ne na Akinci, aka bai wa matukan jiragen yakin kasar umarni na yin luguden wuta ga majalisar dokokin kasar da kuma fadar shugaban kasa a daren 15 ga watan Yuli na 2016.