Turkiyya na shirin afka wa Kurdawa | Labarai | DW | 15.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya na shirin afka wa Kurdawa

Shugaba Racep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya ya yi bayyana yiwuwar afka wa mayakan Kurdawa a arewacin Syria, yankin da ke da iyaka da kasar Turkiyya.

A jawabin da ya gabatar wanda aka watsa ta tashoshin talabijin na kasar, shugaba Erdogan na kasar Turkiyya, ya ce za a ci gaba da kai manyan hare-haren kan mayakan na Kurdawa a garin Afrin a 'yan kwanakin nan. Wani kakakin rundunar mayakan Kurdawa ta YPG Rojhat Roj, ya ce za su kare iyakokinsu ala kulli halin daga duk wani farmakin da gwamnatin Turkiyya zata iya kai masu.

A ranar Lahadin da ta gabata ma dai an yi wani artabu tsakanin mayakan Kurdawan da sojin Turkiyya, inda wani mayakin Kurdawa guda ya rasa ransa, wasu tarin fararen hula kuwa suka jikkata. Shugaba Erdogan ya kuma yi wa kasashen yamma musamman Amirka kashedi, bayan sanarwar da Amirkar ta yi na samar da dakaru dubu 30 da suka hada da Kurdawa, a arewacin kasar Syria.