1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: An fidda hoton karshe na Khashoggi

Ahmed Salisu
October 9, 2018

Jaridar Washington Post ta wallafa wani hoto wanda ta ce shi ne karshe da aka dauka na dan jaridar Saudiyya din nan Jamal Khashoggi da ya yi batan dabo tun bayan da ya shiga ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyya.

https://p.dw.com/p/36Cdk
Jamal Khashoggi saudischer Journalist
Hoto: picture-alliance/dpa/V. Mayo

Hoton da jaridar ta wallafa ya nuna Mr. Khashoggi a lokacin da ya ke kokarin shiga ofishin jakadacin na Saudiyya din a birnin Santambul kuma ta ce wani da ke kusa da wadanda ke bincike kan bacewarsa ne na aike mata da hoton.

Hukumomi a Turkiyya da abokan Khashogi din sun ce suna kyautata zaton an kashe dan jaridar ne a cikin ofishin jakadancin kasarsa lokacin da ya shiga don neman takardun da za su bashi dama wajen auren budurwarsa 'yar kasar Turkiyya sai da Saudiyya din ta musanta wannan zargi.

Jamal Khashoggi dai na daga cikin wanda ke kan gaba wajen sukar hukumomin Saudiya musamman ma manufofin Yarima mai jiran gadon mulkin kasar Muhammad Bin Salman.