Turkiya ta yi ruwan bama-bamai kan IS | Labarai | DW | 25.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta yi ruwan bama-bamai kan IS

A jawabin da ofishin firaministan kasar ta Turkiya ya fitar ya nunar da cewa harin jirgin yakin ya samu rumbun ajiyar makamai da motoci na dakarun PKK.

Türkei Luftwaffe Kampfflugzeug F-16

Jirgin yakin Turkiya

A karo na biyu a ranar Asabar din nan dakarun sojan kasar Turkiya sun sake ruwan bama-bamai a yankunan da a ke saran matattara ce ga mayakan sakai na IS a Siriya, sannan sun kai sabbin hare-hare ga sansanoni na mayakan sakai na Kurdawa a gabashin Iraki.

Wadannan hare-hare kan mayakan na IS da mayakan na Kurdawa bangaren PKK wadanda dukkansu kasar ta Turkiya ke adawa da su, na zuwa ne mako guda bayan da kasar ta Turkiya ta fiskanci tashin hankali na harin bama-bamai da ya jawo asarar rayuka, abinda take alakatanwa da kungiyoyin wajen kitsa shi.

A cewar wani jami'i na kamfanin dillancin labaran Anatoliya a Turkiya jirgin yakin mai lamba F16 ya tashi ne daga Kudu maso Gabashin birnin Diyarbakir ya je ya kaddamar da hare-hare kan sansanonin na mayakan IS da PKK kana ya dawo inda ya tashi da safiyar Asabar din nan ba tare da samun wata matsala ba.

A jawabin da ofishin Firaministan kasar ta Turkiya ya fitar ya nunar da cewa harin jirgin yakin ya samu rumbun ajiyar makamai da motoci da ma wuraren kwana na mayakan na PKK sai dai bai bayyana wuraren da harin ya shafa ba a bangaren na IS a Siriya.