Turkiya ta tsare wasu ′yan IS 21 | Labarai | DW | 10.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta tsare wasu 'yan IS 21

Mahukuntan kasar Turkiya sun sanar da tsare wasu mutane 21 da suka hadar da 'yan kasashen ketare uku da suke zargin 'yan kungiyar ta'addan IS ne.

Ana zargin mutanen da 'yan sandan suka cafke da sanyin safiyar yau yayin wani samame da suka kai a birnin Istanbul da gundumar Sanliurfa da ke kusa da kan iyakar kasar da Siriya da kudancin gundumar Mersin da kuma gundumar Kocaeli da ke gabashin birnin Istanbul, da taimakawa kungiyar ta IS wajen samun sababbin mambobi da suke hurewa kunne daga kasashen Turai. Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan kasashen wajen da aka kama cikin mutanen 21 da ba a riga an bayyana daga inda suka fito ba, an cafke su ne a yayin da suke kokarin tsallakawa kasar Siriya daga Turkiyan.