1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta tarwatsa gangami a Istanbul

Mouhamadou Awal BalarabeMay 1, 2015

'Yan sandan Turkiya sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa ma'aikatan kasar da suka hallara a dandalin Taksim don bayyana koke-kokensu tare da karrama mazan jiya.

https://p.dw.com/p/1FIm4
1. Mai Proteste Ausschreitungen in Istanbul
Hoto: Reuters/M. Sezer

'Yan sandan kwatar da tarzoma na kasar Turkiya sun yi amfani da hayaki da mai sa hawaye da kuma ruwa mai sa kaykayi, wajen tarwatsa mutane sama da dubu guda da suka hallara a dandalin Taksim a ke Istanbul, domin gudanar da bikin ranar ma'aikata ta duniya.

Kungiyoyi kwadago da dama da kuma jam'iyyun adawan wannan kasa ne, suka yi kira ga ma'aikata da su gudanar da gangami da nufin karrama wadanda suka rigamu gidan gaskiya a wannan dandali shekaru 3 ke nan da suka gabata. Sai dai kuma gwamnatin ta Ankara ta riga ta haramta duk wani gangami ko zanga-zanga a dandalin na taksim tun bayan tayar da kayar baya na kwanakin baya.

Mutane 134 ne dai 'yan sanda suka kama bayan harbi da suka sha da kwalabe. Sannan kuma jami'an na tsaro sun yi wa dandalin na Taksim kawanya don hana masu zanga-zanga kutsawa ciki.