1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta saki dan jaridar nan Bajamushe

Yusuf Bala Nayaya
February 16, 2018

Kotu a Turkiya ta bayyana saki na dan jaridar nan Bajamushe mai asali da Turkiya Deniz Yücel abin da ke zuwa bayan shekara guda ana tsare da shi bisa alakantashi da yada farfaganda ta 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/2soFJ
Deniz Yücel Journalist in der ZDF Talkshow maybrit illner am 26 11 2015 in Berlin
Hoto: Imago/Müller-Stauffenberg

Gidan jaridar da yake aiki a Jamus Die Welt, ya bayyana sakin dan jaridar a shafinsa na Twitter a wannan rana ta Jumma'a inda ya bayyana samun wannan bayanai daga lauyan da ke kare dan jaridar. Ya ce an saki dan jaridar Yücel mai shekaru 44 bayan tsare shi ba tare da yi masa shari'a ba, lamarin da ya kara rura wutar rikici tsakanin mahukuntan Berlin da Ankara da ke zama kawayen juna a kungiyar tsaro ta NATO.

Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel ya fada wa manema labarai a birnin Munich cewa suna cike da fata na ganin dan jaridar nan ba da dadewa ba ya bar kasar ta Turkiya.