Turkiya ta lashi takobin daukar mataki kan Qurdawa | Siyasa | DW | 22.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Turkiya ta lashi takobin daukar mataki kan Qurdawa

Kasar Turkiya ta shiga wani tsaka mai wuya na game da shirinta na kaddamar da babban hari kan Qurdawa yan tawaye dake arewacin Iraki,bayan kashe sojojin Turkiya 17 da sukayi,yayinda a hannu guda Amurka ke neman Turkiya ta dan dakata

default

Firaministna Raceb Tayyib Erdogan yanzu haka yace ya amince ya baiwa Amurka yan kwanaki kadan lafin kaiwa wannan hari,yayinda Amurkan ke kokarin kare duk wani matakin soja da Turkiya take son dauka a arewacin Iraki.Sai dai kuma ya bukaci Amurkan da ta gaggauta daukar mataki kan Qurdawa ya aware.

Harin mafi muni da yan kungiyar PKK suka taba kaiwa tun fiye da shekaru 10 ya zo ne kawanaki hudu bayan majalisar dokokin Turkiya ta amince da tura dakarun kasar su yaki yan kungiyar ta PKK dake arewacin Iraki.

Gwamnatin Turkiya ta kiyasta cewa akalla yan tawaye 3,000 ne suke yankin suna masu neman warewa daga Iraki.Ankara a nata bangare ta tura sojoji 100,000 da tankunan yaki da helikoptocin yaki.

Kasar Amurka abokiyar kawancen Turkiya a NATO tana jin tsoron cewa duk wani matakin soja daga bangaren Turkiya zai kara kawo rudani a yankin,baa ga yankin kadai ba har ma da sauran kasashe da abin ya shafa kamar dai yadda sakataren tsaro na Amurka Robert Gates ya baiyana.

“daukar babban dauki a bakin iyaka kasashen zai saba da bukatun Turkiya da ma na Amurka da kuma Iraki kanta”

A wajen wani taro da maema labarai firaminista Raceb Tyyib Erdogan na Turkiya ya kasar ta Turkiya tana son ganin Amurka ta dauki kwararan matakai kan yan kungiyar PKK.Inda yace ba zasu amince da amince da sako sako da shugaban Irak yakeyi akan yan awaren Qurdawa ba.

“halin ko in kula da shugaba jalal talabani yake nunawa yan taadda ba zai samu karmuwa a gurin mu ba,babu wani abinda zamu tattauna da duk wata kasa da bata dauku kungiyar PKK a matsayin kungiyar yan taadda ba”

A daren jiya lahadi ofishin shugaba Abdullahi Gul ya fito da wata sanarwa da ke cewa Turkiya zata yi duk iyaka binda zata iya wajen yaki da taaddanci.Sanarwar tace yayinda Turkiyan zata mutunta iyakokin kasar Iraki,amma kuma ahannu guda zata kare nata yancin,da dokokinta da kuma yan kasarta.

Turkiya dai tuni take kira ga hukumomin Amurka da Iraki da su dauki mataki kan yan tawayen na PKK,da shugabbninsu da ake ganin sun kafa sansanoninsz a yanki mai tsaunuka na arewacin Iraki,amma ba tare da an ga wani abin azo a gani a bangaren Amurka da Irakin ba.

A nata bangare gwamnatin Iraki tace tana daukar matakai na kawo karshen abinda ta kira harkokin taaddanci na yan tawayen Qurdawa.

Sai dai kuma shugaban Qurdawa na Iraki Masoud Barzani yace yankinsu mai cin gashin kansa zai kare kansa idan dakarun Turkiyan suka kutsa ciki.

Shugaban Iraki jalal talabani dai ya tunzura Turkiya ne da kalamn da yayi na cewa ba zasu taba mika wani ba Qurde ga Turkiya ba,ko da kuwa kyanwa ce ta Qurdawa.