Turkiya ta janye jakadanta a Jamus | Labarai | DW | 02.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta janye jakadanta a Jamus

Tukiyya ta janye jakadanta da ke Jamus tare da aike wa jakadan Jamus din a Turkiyya da sammaci biyo bayan ayyana kisan Armeniyawa da kisan kiyashi da majalisar dokokin Jamus ta yi.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shigaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shigaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Majalisar dokokin ta Jamus ta Bundestag dai, ta ayyana kisan Armeniyawan da Turkiya ta yi a yayin yakin duniya na daya da kisan kiyashi. Dama dai shugaban kasar ta Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya yi ikirarin cewa muddin majalisar dokokin ta Jamus ta amince da kudirin, to kasashen biyu na iya fuskantar nakasu a alakar da ke tsakaninsu. A nata bangaren shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kare matakin majalisar dokokin, koda yake ta ce a shirye take ta shiga taimaka wajen tattaunawa tsakanin Turkiyyan da Armeniya. Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag dai ta amince da kudirin da ya tabbatar da kisan kiyashin da Turkiyya ta yi wa Armeniyawa da wasu Kiristoci a karkashin daular Usmaniya.