Turkiya na shirye shiryen karbar makaman kariya daga NATO | Labarai | DW | 05.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya na shirye shiryen karbar makaman kariya daga NATO

Tun bayan da rikicin kasar Siriya ya dauki wani sabon salo inda bangarorin biyu ke amfani da manyan makamai,kasar Turkiya ke nuna fargabanta.

default

Irin makaman kariyar da Turkiya ke bukata

A jiya Juma'a ne aka yi bukukuwan karbar makamakan kariyar da kungiyar Nato ta yi arkawarin baiwa kasar Turkiya a wani matakin kare kanta daga makaman gwamnatin Siriya. Gwamantin Ankara dai ta nuna fargabanta matuka a dangane da yadda makamai ke fadawa a kasarta daga Siriya a yakin da ake ci gaba da yi tsakanin sojojin gwamnatin Asad da 'yan tawayen. Kasasashen biyu na tarayar iyakar da ta kai kimanin kilometa 900. Sojojin Amurka ne za su kula da shirye shiryen gwajin makaman nan gaba ,yayin da su ma a nasu bangare,kasashen Amurkan da jamus da kuma Holland suka yi arkawarin taimakawa kasar da karin wasu makaman kariya tare da aikawa da sojojin da adadinsu zai kai 400 daga kowace daga cikin kasashen ukku. Tuni dai fadar Pentagone ta Amurka ta ce ita dai a shirye ta ke ta tura da tata gudunmuwar nan da karshen mako mai zuwa.

Mawallafi: Issoufou Mamane

Edita : Usman Shehu Usman