Turkiya ba ta kawad da yiwuwar amfani da soji kan Ƙurdawa ba | Labarai | DW | 28.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ba ta kawad da yiwuwar amfani da soji kan Ƙurdawa ba

Kasar Turkiya ta sake yiwa mayakan kungiyar Kurdawa ta PKK kashedi. Ministan harkokin wajen Turkiya Ali Babacan ya jaddada cewa har yanzu suna nazarin yiwuwar amfani da soji akan sansanonin ´yan tawayen PKK dake arewacin Iraqi. A halin da ake ciki ministan na wata ziyara ce a kasar Iran. Gwamnatin kasar Iran dai na adawa da duk wani kutse sojin Turkyia a cikin Iraqi. Shugaba Mahmud Ahmedi-Nejad ya ce kamata yayi Turkiya ta tattauna da kungiyar PKK.