Turkiya: An kama magoya bayan Gulen 1000
April 26, 2017Jami'an 'yan sanda a Turkiya bayan aikin sumame da suka gudanar sun kama mutane 1000 bisa zargin alaka da babban malamin nan dan asalin kasar da ke zaune a Amirka Fethullah Gulen. An dai mika takardun sammaci ga kimanin mutane 2,200 da ake zargi da alaka da shehin malamin kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya bayyana.
A cewar kamfanin dillancin labaran Anadolu mutane 1,013 ne kawo yanzu aka kamasu, kamen da ke zama daya cikin mafiya girma a 'yan watannin nan.
Ministan harkokin cikin gidan Turkiya Suleyman Soylu ya ce aikin simamen da aka kaddamar mataki ne da ke zama babba a kokari na dakushe magoya bayan na Gulen: "Yanzu an kama malaman sirri 1,009 a larduna 72 , wannan babbar nasara ce ga Jamhuriyar Turkiya, muna fama da matsalar 'yan gudun hijira da 'yan ta'adda ga kuma wata matsalar saboda banbancin yanki."