Turai za ta dauki nauyin masana yanayi | Labarai | DW | 15.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turai za ta dauki nauyin masana yanayi

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi kira ga kasashen Turai da su dauki nauyin kungiyar kwararru a fannin sauyin yanayi ta MDD ta GIEC ko IPCC bayan da Amirka ta janye daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris.

 

Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a wannan Laraba a taron sauyin yanayi na duniya na COP 23 da ke gudana a nan birnin Bonn wanda a yau shugabannin kasshen duniya suka halarta inda za su share kwanaki biyu suna gabatar da jawabai. Shugaba Macron dai ya ce Faransa za ta kasance a sahun gaban samar da wadannan kudade inda ya yi kira ga sauran kasshen na Turai yana mai cewa:

" Ina fatan ganin akasarin kasashen Turai sun bamu hadin kai ga cike gibin kudaden da Amirka ke zuba wa wannan kungiya, kuma ina mai tabbatar maku da cewa daga farkon shekara 2018 kungiar ba za ta sake fuskantar matsalar kudin tafiyar da aiki nata ba."

Kungiyar kwararrun kan sauyin yanayi ta MDD  na aikin nazari tare da bayar da shawarwari ga shugabannin duniya kan girman matsalar sauyin yanayi da kuma irin matakan da ya dace su dauka domin tunkarar matsalar.