Turai na tattauna batun ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 09.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turai na tattauna batun 'yan gudun hijira

Da wannan tattaunawar dai, ministocin na fatan samun mafita mai kwari domin shawo kan matsalar.

Yawan masu gudun hijira ta yankin Balkan ya karu sosai a yayin da ministocin cikin gidan Turai ke shirin tattauna hanyoyin shawo kan wannan matsalar da take kokarin ta gagari kundila. Ministocin za su gana ne a wannan litinin da rana a birnin Brussel da fatan samun mafita mai kwari bisa fargaban da ake yi na cewa wata kila Jamus ta rufe iyakokinta, abin da ka iya janyo matsala ga kasashen da ke kan hanyar da 'yan gudun hijirar ke bi.

Jamus ce kasar da yawancin 'yan gudn hijirar ke hankoron zuwa a yanzu haka, kuma ta riga ta dauki dimbin 'yan gudun hijira. Sloveniya a matsayinta na kasa mafi kankanta a kan hanyar da masu gudun hijrar ke bi, ita kanta ta yi rajistan mutane dubu biyar da rabid aga yammacin lahadi zuwa litini kadai. Bakin da suke bin wannan hanya dai yawancinsu daga kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya ne wadanda ke fama da yaki.