Turai da Girka sun cimma matsaya. | Labarai | DW | 13.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turai da Girka sun cimma matsaya.

Bayan da suka kwashe sa'o'i 17 suna tattaunawa bangarorin biyu sun cimma matsaya na bai daya kuma sun ce Girka na nan a kungiyar EU ba inda za ta.

Shugabannin Turai sun cimma matsaya na bai daya dangane da batun ceto Girka. Shugaban majalisar zartarwar Turan Donald Tusk ne ya bayyana hakan da safiyar litini, lokacin wani taron manema labaran da ya yi tare da shugabanin kungiyar da na rukunin kasashen da ke amfani da euro. Sai dai sun ce sabon shirin ya kunshi tsauraran matakai wadanda tilas ne majalisar dokokin Girkar ta amince da su, amma kuma Girka na nan daram a EU.

Wannan na zuwa ne bayan da shugabannin kasashen Jamus Angela Merkel da Francois Hollande na Faransa da shugaban rukunin kasashen kungiyar tarrayar Turai, Donald Tusk da kuma firaministan Girka Alexis Tsipras suka gabatar da wani sabon tayi na sauye-sauyen tattalin arziki domin ceton Girka, wanda suka dauki lokaci mai tsawo suna nazarin shi.

Tun farko a taron da aka kwashe sa'o'i 14 ana yi a jiya na mnistocin kudi na kungiyar ta EU a Brussel, an samu rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen dangane da rawar da hukumar bada lamuni ta duniya IFM za ta taka a cikin shirin na ceton tattalin arzikin Girka, da kuma tsarin da aka yi na sayar da hannayen jari na kamfanonin gwamnatin na Girka.