1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai da Afirka sun yi zama kan 'yan gudun hijira

Gazali Abdou Tasawa
August 29, 2017

Shugabannin bakwai na wasu kasashen Turai da Afirka sun yi zama a birnin Paris na kasar Faransa kan 'yan gudun hijira. Kasashen Turai sun jinjinawa kokarin da kasashen Afirka ke yi wajen dakile kwararar 'yan gudun hijira

https://p.dw.com/p/2izO6
Italien Flüchtlinge werden von Hilfsorganisation Sea-Eye gerettet
Hoto: picture alliance/dpa/NurPhoto/C. Marquardt

Shugabannin bakwai na wasu kasashen Turai da Afirka sun yi zama a birnin Paris na kasar Faransa kan batun matsalar 'yan gudun hijira. Makasudin taron dai shi ne jaddada goyon bayan kasashen Turai kan kokarin da kasashen Nijar da Chadi da Kuma Libiya ke yi wajen dakile kwararar 'yan gudun hijira zuwa Turai da kuma nazarin hanyoyin taimaka masu domin inganta matakan nasu.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ne ya kira wannan taro na birnin Paris inda ya gayyato Shugaba Idriss Deby na Chadi da Mahamadou Issoufou na Nijar da kuma shugaban gwamnatin hadin kai na kasar Libiya Fayez al-Sarraj daga bangaren Afirka da kuma Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Paolo Gentiloni na Italiya da Mariano Rajoy na Spain da kuma kantomar harkokin wajen ta Kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini daga  bangaren Turai.

Frankreich Migrationsgipfel in Paris
Shugabannin Turai sun jinjinawa Afirka wajen kokarin dakile bakin haureHoto: Reuters/T. Camus

Shugabannin dai za su yi bitar inda aka kwana a game da batun yaki da kwarar bakin haure da bangarorin biyu suka cimma a karkashin wasu yarjejeniyoyi wadanda suka tanadi taimaka wa wadannan kasashen na Afirka da kudi tsaba domin dakile kwararar bakin haure 'yan Afirka da ke ratsowa ta wadannan kasashe zuwa Turai. Wani batun da wannan taro na birnin Paris zai duba shi ne na shirin kafa cibiyoyin karbar 'yan gudun hijira da yi masu rijista a kasashen na Nijar da Chadi da kuma Libiya matakin da kasashen uku ke yin dari-dari da shi.

Kasar Italiya wacce matsalar 'yan gudun hijirar ta fi shafa wacce 'yan gudun hijira sama da dubu 600 suka shigo cikinta daga kasar Libiya a shekaru uku na baya bayan nan ta yi barazanar haramta wa jiragen ruwa na 'yan kasashen ketare da ke ceto 'yan gudun hijira a teku izinin shiga tashoshin jiragen ruwanta. Batun da Italiyar ke son tattaunawa da mahukunatn kasar ta Libiya a wurin wannan taro da zummar fito da sabbin shawarwari na tunkarar wannan batu.