1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farashin man fetur zai karu a Tunisiya

Zulaiha Abubakar MNA
June 1, 2018

Kasar Tunisiya ta sanar da yin karin farashin kudin mai nan ba da dadewa ba a daidai lokacin da ta jingene batun karin albashin ma'aikatan kasar don samun cika sharadan Asusun bada lamuni na Duniya.

https://p.dw.com/p/2yoCM
Tunesien Präsident Beji Caid Essebsi
Shugaban Tunisiya Mohamed Beji Caid EssebsiHoto: picture-alliance/dpa

 

Matakin tsuke bakin aljihun da gwamnatin kasar ta dauka tun bayan hambarar da shugabancin Zine El-Abidine Ben Ali a shekara ta 2011 na fuskantar bore daga babbar kungiyar kwadago ta kasar, wadanda suke korafin matsin tattalin arziki ya addabi al'umma musamman ma ma'aikata.

Cikin wannan makon ne tawagar wakilan Asusun bada Lamuni na Duniya wato IMF suka ziyarci kasar ta Tunisiya don ganawa da mahukuntan kasar.