Tunisiya za ta ci gaba da matakan tsimi | Labarai | DW | 17.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tunisiya za ta ci gaba da matakan tsimi

Gwamnatin Tunisiya ta yi alkawarin ci gaba da matakin tsuke bakin aljihu wanda ya janyo zanga-zanga da tashin hankali a kasar baki daya.

Gwamnatin Tunisiya ta bayyana cewa babu gudu babu ja-da-baya game da matakin tsuke bakin aljihu wanda ya janyo zanga-zanga da tashe-tashen hankula a kasar da ke yankin arewacin Afirka. Firaminista Youssef Chahed ya bayyana haka a birnin Tunis fadar gwamnatin kasar inda ya ce matakin shi ne kadai ya rage idan har gwamnatin ta bukatar inganta tattalin arzikin kasar.

A makon jiya tashin gwauron zabi na farashin kayayyakin bukatu ya harzuka 'yan kasar ta Tunisiya musamman matasa wadanda suka fito kan tituna, abin da ya janyo mutuwar mutum guda, yayin da wasu jami'an tsaro kimanin 100 suka samu raunika. Kiyasi ya nuna kashi 15 cikin 100 na 'yan kasar suna zaman kashe wando, kamar yadda alkaluman hukumomi suka tabbatar.