Tunisiya ta shiga rudani bayan kisan jagoran adawa | Siyasa | DW | 07.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tunisiya ta shiga rudani bayan kisan jagoran adawa

Kisan madagun 'yan adawar kasar Tunisiya, Chokri Belaid ya sa Firaministan kasar, Hamadi Jebali rusa gwamnati da kiran zabe cikin gaggawa.

Mutane daga bangarorin rayuwa daban-daban sun nuna fushinsu da kisan da aka yi wa madugun 'yan adawar kasar ta Tunisiya, Chokri Belaid ranar Laraba da ta gabata kusa da gidansa sakamakon harbin bindiga da aka masa a kai da kirji.

Ga abun da daya daga cikin masu zanga zangar ke cewa kan kisan da aka yi wa maudgun 'yan adawan kasar ta Tunisiya, Chokri Belaid.

"Dukanmu 'yan Tunisiya ne. Dama da hagu duk daya ne. Amma hakab bai dace ba, ba haka ya kamata ya kasance a wannan kasa ba."

Wa ke da alhakin kashe Belaid?

Wannan shi ne karon farko cikin shekaru biyar da dan siyasar Tunisiya ya fuskanci irin wannan hali. Wannan kisa da aka yi wa Belaid da yammacin Lara da zai halarci wata mahawara ta tashar talabijin bisa kisan 'yan siyasa. Akwai 'yan adawa masu yawa da ke asibiti. Iyed Dahmani mai tsaka-tsakin ra'ayi ya dora alhakin wannan kisa ta dan adawa akan gwamnati ta jam'iyyar Ennahdha mai ra'ayin Islama.

"Wannan kisa ne na siyasa, cikin kasar da aka aiwatar da juyin-juya-hali."

Masu zanga-zangar cikin kasar ta Tunisiya kan kisan wannan kusa na 'yan adawa, Chokri Belaid mai sukar jam'iyya mai mulki, sun kuma rera wakokin juyin-juy- hali.

Daya daga cikin masu wannan zanga-zangar ya bayyana damuwa da wannan yanayi:

"Wannan gwamnati za ta janyo mana halin kaka-ni-kayi ko kuma wani sabon juyin-juya-hali. Mun zabe su ne da tunanin cewa su masu tsoron Allah ne. Amma babu abun da ya dame su sai rarraba mukamai. Allah ya kare mana wannan kasa."

Marigayi Chokri Belaid, ya yi suna wajen sukar gwamnatin kasar ta Tunisiya da jam'iyyar Ennahdha mai mulki. Mohammed Souissi wanda malamin jami'a ne ya san Belaid tun lokacin suna makaranta:

"Belaid ya kawo sabbin ra'ayoyi. Ennahdha da 'yan Salafi sun sa masa ido sun bi kadinsa. Kuma sun saka tunaninsa cikin zukatansu. Sun dauki hankalinsu sun saka kan wanda ke zama musu barazana. Shi Belaid mutun ne wanda ya saka mutane suka fara tunani wannan kuma shi ne abun da Tunisiya ke bukata, kuma kasar ta farfado."

Kiran zabe cikin gaggawa

Tunisian Prime Minister Hamadi Jebali speaks during a press conference on the result of consultations with the political parties on a government reshuffle on January 26, 2013 in Tunis. Ruling Islamist party Ennahda, first said that a reshuffle was 'imminent' last July to enlarge the current coalition that also includes two secular centre-left parties, Ettakatol and President Moncef Marzouki's Congress for the Republic. AFP PHOTO / FETHI BELAID Sufi leaders soretent the mausoleum of Sidi Bellahsen Chadly after having completed their weekly ritual on January 26, 2013 in Tunis. The Tunisian government has promised to day measures 'emergency' to protect Sufi shrines covered by dozens of attacks, an announcement Saturday called 'positive' by the Union but tradive Sufi Tunisia accuses Salafi factions of these rampages . AFP PHOTO / FETHI BELAID (Photo credit should read FETHI BELAID/AFP/Getty Images)

Hamadi Jebali

Firaministan kasar Tunisiya, Hamadi Jebali ya yi kiran zabe cikin gaggawa, wasu sa'o'i kadan bayan kisan madugun 'yan adawan kasar abun da ya haifar da zanga-zanga.

Yayin jawabi ta tashar talabijin, Firaminista Jebali ya ce zai kafa gwamnatin da ta kunshi kwararru ta wucin gadi, zuwa lokacin da za a gudanar da zabuka. Tuni shugaban kasar ta Tunisiya, Moncef Marzouki ya yi tir da wannan kisa. A kasar ta Tunisiya aka fara juyin-juyin-hali kasashen Larabawa cikin shekara ta 2011, inda masu zanga-zanga suka kawo karshen gwamnatin Zine el-Abidine Ben Ali.

Za a iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.

Mawallafi: Sara Mersch/Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas

Sauti da bidiyo akan labarin