Tunawa da ranar yaran Afirka ta 16 ga watan Yuni | Siyasa | DW | 16.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tunawa da ranar yaran Afirka ta 16 ga watan Yuni

A yayin da ake bukin tunawa da ranar yaran Afirka, Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya fitar da sakamako kan adadin yara 'yan gudun hijira na Burundi.

Binciken ya nunar cewa, a kalla kashi 83 cikin 100 na mutanen da rikicin kasar Burundi ya tilasta wa gudun hijira, dukananinsu kananan yara ne. Kuma a halin yanzu suna fama da dumbun matsaloli na rayuwa inda kawo yanzu aka samu a kalla mutane 32 da suka rasa rayukansu a sansanin 'yan gudun hijar sakamakon barkewar annobar cutar Kwalara, abun da ke zaman wata babbar barazana ga rayuwar akasarin yaran da ke tsugunne a wannan sansani kamar yadda David Wright, Darectan kungiyar Save the children reshen gabashin Afirka ya sanar a firar da ya yi da tashar DW.

Kindersoldaten - Burundi

Yara na fiskantar matsaloli a Burundi.

"Akwai a kalla yara dubu da basa tare da iyayensu cikin wannan sansani da suka fito daga kasar Burundi, kuma basa cikin kyawawan yanayi. Akwai babbar matsalar karancin abinci a kasar ta Burundi kuma yanayin da yaran da ke cikin wannan sansani suka tsinci kansu sakamakon karancin abinci ya ta'azzara sosai. "

Lalle akasarin yaran dai da ke cikin sansanonin 'yan gudun jihirar da ke kasashen Ruwanda da Tanzaniya na zau ne ba tare da iyayen su ba. To ko wane mataki ne masu kula da 'yan gudun hujirar ke dauka musammen ma dangane da kwantar da hankullan yaran ganin irin mawuyacin halin da suke ciki a dai dai wannan lokaci. Tambayar da DW ta yi wa David Wright, Darectan kungiyar Save the children reshen gabashin Afirka.

" Babban burin dai, shi ne na rajistar yaran da basa tare da iyayensu, sannan kuma a basu tallafi na tufafi, da samar musu da abincin da ya dace, kuma duk hakan sai da masu ayyukan sa kai da zasu iya bin diddigin wadannan yara sau da kafa tare da taimaka wa wajan gano iyayensu idan har iyayen na su na da rai."

To duk da haka ko wadannan kungiyoyi na samun nasarar baiwa wadannan yara kariya ta hanyar kula da su sosai ko kuma akwai wasu matsaloli da suke fuskanta sakamakon hakan. Sai David Wright na kungiyar da ke kula da yara kanana ta Save the children reshen gabashin Afirka ya ci gaba da cewa...

'Yan gudun hijirar Burundi na bukatar agaji.

" Lalle kula da 'yan gudun hijira a kalla dubu goma ba karamin aiki ba ne, kuma matsalar a nan ita ce akwai matsaloli da dama irin wannan a fadin duniya, kuma wannan matsala ta wadannan 'yan gudun hijira na Burundi ba ta dauki hankalin kasashen duniya ba, don haka muddin ba'a samu tattara kudadan da suka dace ba, to ba shakka za'a fiskanci matsololi masu yawa nan gaba domin a kullu yaumin ana samu 'yan gudun Hijira a kalla 100 zuwa 200 da ke zuwa kasar Ruwanda ko Tanzaniya."

A ranar Litinin ce dai sanarwa karshen taron shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka da ya gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu ta tsayar cewa kungiyar zata tura kwararru ya zuwa kasar ta Burundi domin sa ido ga batun kwance damarar gungun mutanen da ke dauke da makammai masu goyon bayan jam'iyyun siyasa a kasar, a kokarin da ake na ganin an kawo karshen tashe-tashen hankulla a wannan kasa wanda kuma kawo yanzu ya sanya dubban yara cikin matsanancin kuncin rayuwa.

Sauti da bidiyo akan labarin