Tunawa da juyin juya halin kasar Tunisiya | Labarai | DW | 14.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tunawa da juyin juya halin kasar Tunisiya

A yau ne dubun dubatan 'yan kasar Tunisiya suka fito kan titunan birin Tunis domin bikin tunawa da lokacin da aka hambarar da tsohon shugaban kasar Zine El Abidine Ben Ali.

'Yan Tunusiyan dai sun hallara ne a dandalin Habib Bourguiba da ke a tsakiyar birnin Tunis, a inda nan ne guguwar neman sauyin ta samo a sali shekaru biyar da suka gabata.

Ga mafi yawan 'yan Tunisiya dai, juyin-juya halin wani al'amari ne da dukkanin 'yan kasar za su yi murna da shi, a yayin da wasu ke ganin juyin-juya halin ba abinda ya janyo musu sai tashin farashin kayyakin amfanin yau da kullum.

Tsohon shugaba Ben Ali ya sauka daga gadon mulkin Tunisiya ne, a shekara ta 2011 bayan dubban 'yan kasar sun fito kwansu da kwarkwata, domin nuna kin jinin mulkin sa daya shafe shekaru 23 yana yi, inda kuma hakan ya tilasta masa yin gudun hijira zuwa kasar Saudiya.