Tuhumar sojoji da tallafawa ta′addanci | Siyasa | DW | 10.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tuhumar sojoji da tallafawa ta'addanci

Rundunar tsaron Najeriya ta bayyana kame yayanta da take zargi da hannun wajen saida makamai ga kungiyar Boko haram

Ta dai dauki tsawon lokaci tana kokari na wankan tsarki a tsakanin man'yan hafsoshin da take zargi da karkatar da kudaden yakin ta'addanci a cikin a Nageriya, yanzu kuma hankalinta na karkata ga kananan sojojin da take zargi da kokari na zagon kasa a cikin yakin, a bangaren rundunar tsaron kasar da ta ce babu gudu babu jada baya a neman nasarar yakin.

Tun a farkon wannan mako ne dai sojojin suka ce suna ganin akwai alamar da biyu yanda wasu kananan hafsoshinsu suka yi sakancin kyale kai wani mugun harin da ya hallaka jamaá da daman gaske a kauyen Dalori dake gefen birin Maiduguri. Kuma tuni rundunar sojan kasar ta karya kumallo tare da cafke wasu sojojinta biyu da take zargi da kokari na sai da makamai ga 'yan kungiyar Boko ta haramun. A fadar kakakin sojan kanar Sani Usman Kuka Sheka.

Sojojin da suka hada da Eric Nwokorie da kuma Macauley Fortune dai, a fadar Usman din an same su da makamai iri-iri da kuma rigunan aikin soja daban-daban a ranar Lahadin 07.02.2016 a tashar motar birnin Yola, helkwatar jihar Adamawa.

Duk da ikirarin nasara a bangaren mahukunta na sisaya ta kasar dai, an dauki lokaci na kwan gaba kwan baya a cikin yakin da ke kallon cigaban hare-hare a bangaren 'yan kungiyar ta Boko ta Haram. To sai dai kuma sake kallon tsaf din da fitar da sababbi na dabaru a bangaren rundunar ne dai, ke zaman sabon fata a bangaren sojojin da ke da burin kai karshen yakin a cikin sauri.

Ko bayan shanun gwamnan dai, a har ila yau rundunar sojan ta kuma bayyana aniyar ta, ta rufe wasu kasuwanni har guda uku a cikin jihohin Borno da Yobe, da ke zaman kafa ga kungiyar na saye da sayarwa yanzu a cewar Usman din.

Ana dai kallon sabbabi na matakan a matsayin abun da ke iya kaiwa ga taunin tsakuwa, cikin gidan sojojin da a baya aka zarga da hadin baki da kungiyar da nufin tabbatar da tsawaitar yakin, da ke cikin shekarunsa na Shida . Abun jira a gani a gani na zaman tasirin taunar tsakuwar a cikin yakin da ko bayan lamushe kasafin kudin kasar na shekaru biyu, ya yi kuma sanadiyar tarwatsa mutane miliyan guda biyu daga matsugunansu.

Sauti da bidiyo akan labarin