Tsugunne ba ta kare ba | Learning by Ear | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Tsugunne ba ta kare ba

Wannan ne Kashi na karshe na shirin Tsaka Mai Wuya kuma za mu ji yadda matasan nan wato Ado da Nasir da Hauwa suka shawo kan matsalolinsu.

Ranar Juma’a (17-11-2015) Zamu kawo muku kashi na karshe na shirinmu na Tsaka Mai Wuya, wanda muka kawo muku a zubi har hudu dangane da rayuwar matasan nan Hauwa, Nasir da Ado wadanda muka bibiyi irin kalubalen da suke fiskanta yau da kullun. Mun dai ji irin matsalolin da Hauwa da Nasir suka rika fiskanta a rayuwar aure musamman saboda kyawar cutar da ya ke dauke da ita, kuma mun ga yadda al’ummar Makera ta shiga wani yanayi sakamakon ambaliyar ruwan da ta ci mutane. Mahaifin Ado na daga cikin wadanda ba a gani ba, anya za’a samo bakin zaren kuwa? Sai ku kasance tare da mu dan jin yadda za’a karasa….taken shirin dai shi ne – „Dan marayan zaki"

Sauti da bidiyo akan labarin