Tsugune ba ta kare ba a Ukraine | Labarai | DW | 05.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsugune ba ta kare ba a Ukraine

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya sanar da cewa Rasha na kokarin kwace iko da yankin gabashin kasarsa.

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya cika shekara guda a mulki

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya cika shekara guda a mulki

Poroshenko ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai da ya gudanar a bikin cikar sa shekara guda a kan karagar mulkin Ukraine din, inda ya ce bai ga dadlilin ci gaba da karya ka'idojin yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma ba in har ba Rasha na son mamaye yankin gabashin kasar ba ne. 'Yan awaren gabashin Uktraine din dai na goyon bayan mahukuntan Moscow kuma suna da karfin iko a yankin. Cikin wannan makon dai an fuskanci fafatwa mafi muni tsakanin dakarun gwamnatin Kiev da kuma 'yan awaren gabashin kasar da ke goyon bayan Rasha duk kuwa da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu a birnin Minsk.