Tsoron yaduwar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Zamantakewa | DW | 16.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tsoron yaduwar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Gwamnatin ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya tabbatar da bullar cutar Ebola a birnin Goma. Karon farko da cutar ta bayyana a birnin mai girma na kasar tun bayan sake barkewar annobar Ebola a watan Agustan 2018.

A wani taro da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta gudanar a Geneva, ta yi nuni da cewar yaduwar Ebola a birnin Goma na gabashinn Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, wani babban ibtila'i ne duba da yawan mutanen birnin sama da miliyan biyu. Haka kuma lamarin ya kasance wanda hukumar ta WHO da kuma gwamnatin kasar Kwango suka yi wa tanadi sannan kuma wannan lamari na daya daga cikin abubuwa masu rikitarwa da ke bukatar nazarin gaggagawa da suka taba fuskanta. Amma duk da haka suna da tabbacin kawo karshen yaduwar cutar a birnin na Goma.

Dr Harouna Djingarey na sashen kula da cututtuka masu yaduwa a ofishin hukumar WHO a gabashin Kwango ya ce matsalar da aka samu ita ce birnin Goma babban gari ne, shi ne babban birnin lardin kuma yana dauke da mutane sama da milyan biyu. A birnin Goma babban filin jirgin sama na kasa da kasa yake, daga nan za ka iya zuwa wasu manyan birane kamar Nairobi na Kenya, Adiss ababa na Habasha, New York na Amirka da saura.

An fara allurar riga kafin ne a birnin Goma a ranar Lahadin da ta gabata bayan wani limamin coci da ya je wa'azi garin Butembo,r ya dora hannunsa a kan mutane marasa lafiya a duk cocin da ya ziyarta, ya kamu da kwayoyin Ebola.  Yanzu haka dai an mayar da shi garin na Butembo domin a yi masa magani inda kuma mutanen da suka shiga mota daya da shi an killace su ana musu allurar riga kafi.

Sai dai duk da kokarin da hukumomin kiwon lafiya suka yi na kwantar da hankalin jama'a da yi masu bayani kan irin matakan da suka dauka, jama'a a birnin na zama a cikin halin dar-dar kamar yadda Dakta Guylain Mvuama babban daraktan gidan asibitin Kyeshero na birnin na Goma ya bayyana.

Hukumomi da kungiyoyin agaji sun yi kokari dakile yaduwar cutar ta Ebola a tsakanin mazauna yankin da ke nuna rashin yarda da ma'aikatan kiwon lafiya.

Zuwa yanzu dai mutane sama da 1600 sun rasa ransu a sakamakon cutar a Kwango.