Tsoron hare-haren Boko Haram a jihar Borno | Siyasa | DW | 24.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tsoron hare-haren Boko Haram a jihar Borno

Rundunar tsaro ta JTF a jihar Borno ta bayyana cewa kungiyar Boko Haram na shirin kai wasu munanan hare-hare ga jami'an tsaro lokacin bukukuwan babbar Sallah.

Rundunar tabbatar da tsaro da zaman lafiya dake jihar Borno wato JTF, ta bayyana cewa kungiyar Boko Haram na shirin kai wasu jerin munanan hare-hare ga jami'an tsaro da fararen hula a lokacin bukukuwan babbar Sallah dake tafe. Rundunar aikin wanzar da zaman lafiya da tsaro a Maiduguri dai tace ta samu wasu bayanai na sirri da ke nuna cewa kungiyar Jama'atu Ahlulsunna Lilda'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram na shrin kai wa jami'a soji da fararen hula hari a lokutan Sallar saboda haka suka gargadi al'umma suyi taka tsan-tsan, kuma su kai rahoton duk abinda basu yarda da shi ba. Sanarwar wanda kakakin rundunar, Laftanar Kanar Sagir Musa ya rattabawa hannu, ta kara da cewa kungiyar gwagwarmayar ta yi hayar wasu ‘yan bindiga daga kasashen waje domin taimaka mata wajen kaddamar wannan jerin hare-hare musamman a jihar Borno.

Wannan sanarwa dai ta tada hankalin mazauna birnin Maiduguri da kewaye, abinda ya tilasta wasu daruruwan jama'a ficewa daga garin domin komawa wuraren da suke ganin sune tudun-na-tsira. A bangare guda kuma jama'a na bayyana fargaba ne kan matakan tsaro da ake dauka domin dakile ayyukan hare-hare da ake fargabar su musamman a yankin Arewa maso gabashin Najeriya. Wani bawan Allah da bai so a bayyana sunan sa ba yayi bayanin irin abinda wannan matakai na jami'an tsaro ya haifar a unguwar su. Masu fafutukar kare hakkin bani Adama dai na ganin wannan mataki bai dace ba, kuma hakan, wanda keta hakkin mutane ne, ya saba da dokokin aikin nasu kamar yadda Muhammad Mailumo ya shaida min.

Ko a wane irin hali kenan al'umma zasu gudanar da bukin babbar Sallah ta bana?Adamu Adamu Mai dala wani mai fashin baki ne a Najeriya.

Nigeria Terror Leiter der Terrorgruppe Boko Haram Sektenführer Imam Abubakar Shekau

Kakakin kungiyar Boko Haram Imam Abubakar Shekau

Yanzu haka kuma al'ummar garin Potiskum na ci gaba da yin tururuwa suna barin garin domin halin da ya shiga da kuma dokar hana yawo da aka kakaba musu duk da bukatar da hukumomin suka yi na neman mutane su kwantar da hankuka kuma su ci gaba da zama a gidajen su. Sai dai al'umomin na ganin ba zasu iya zama ba tunda shugabannin garin ma na tserewa suna barin talakawa cikin kunci da fargaba.

Mawallafi: Al Amin Suleiman Mohammed
Edita Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin