Tsokacin Wole Soyinka kan zaben 2015 | Siyasa | DW | 19.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tsokacin Wole Soyinka kan zaben 2015

Fitaccen marubincin ya tabbatar cewa sojoji na shirin kawar da mulkin farar hula a fakaice, inda ya caccaki mulkin gwamnati mai ci, kana ya ce jagoran 'yan adawa ba abun alfahari ne ba

Tashar DW ta yi hira ta musamman da Wole Soyinka: Tun lokacin da aka sace 'yan matan Chibok daga makarantarsu a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, shahararren marubucin nan na kasar Farfesa Wole Soyinka, ya ce idan dai har ba a gano 'yan matan ba, Najeriya za ta kasance cikin barazana, domin alama ce da ke nuna cewa kasar ba za ta iya tabuka ma kanta komai ba. A wata hira da ya yi da DW, ana kasa da kwanaki 10 kafin zabe, marubucin ya bayyana abubuwa da dama, inda ya yi zargin akwai wata makarkashiyar da ake kullawa wadda ka iya yin tasiri a zabukan masu zuwa.

Wole Soyinka wanda ya taba samun lamba yabo ta Nobel ya dade yana amfani da rubuce-rubucensa wajen yin tsokaci dangane da irin abubuwan da suka shafi siyasar Najeriya. Marubucin ya shaidar cewa ba shi tsammanin za'a gano mafi yawan 'yan matan da aka sace, kuma abin takaicin shi ne, wannan abu ne da zai iya hana mutane sakin jiki su yi kishin kasarsu. To ganin cewa rundanar hadin gwiwa ta musamman ta kudiri anniyar yakar Boko Haram, a ra'ayinka mun fara ganin yunkurin da zai murkushe barazanar ta'addanci baki daya ke nan a Najeriya?.Ya ce: "Zai dauki wata zuri'a guda nan gaba, kafin a ce an shafe wannan akida, domin abu ne da aka riga aka shuka shi a cikin zukatan jama'a, a duk fadin duniya ba a Najeriya kadai ba. Saboda haka a duk sadda na kalli irin nasarorin da jami'an tsaro suka yi yanzu, sai in yi tunanin cewa bai kamata a ce suna irin wahalan da suke yi yanzu da kungiyar Boko Haram ba, idan da an dauki irin matakin da ya dace a lokacin da ya dace. Wannan ce matsalar da ta fi ci mun tuwo a kwarya daga cikin irin matsalolin da muke fiskanta a gwamnatin Jonathan"

To menene ra'ayin marubucin danagane da 'yan takaran da ke fafatawa a zaben mai zuwa? musamman wajen irin rawar da ake hange za su taka ko bayan an kammala zabe? Soyinka ya dade yana bayyana ra'ayinsa dangane da haka kuma har yanzu bai sauya ba:Ya ce: "Irin rawar da gwamnatin Goodluck Jonathan ta taka, abin a yin kuka ne, amma a waje guda kuma madugun adawan yana da irin tarihin da bai kamata wani dan takara ya yi alfahari da shi ba. Ba irin mutumin da za ka daka tsalle ba ne ka ce ka sami amsa, domin akwai abubuwa da yawa da ke faruwa a bayan fage. Ana ta tattaunawa, an kuma ambaci wasu sunaye, ni kai na, na gudanar da bincike dan tabbatar da abubuwan da na ji, wannan ne karon farko da nake magana kan wannan batu a bainal jama'a. Ina magana ne kuma domin na gamsu, kuma ina da hujjoji da ke nuna cewa wasu tsoffin sojoji da ma jami'an tsaro na kokarin yin amfani da tashe-tashen hankalin da ake fama da shi, su ma ture 'yan siyasa, domin su kafa gwamnatin rikon kwarya"

Da yake ya yi maganar cewa akwai yunkurin da ake yi ta bayan fage, na tursasawa 'yan siyasa su yi abin da wasu tsiraru suke so. Furucin ya sanya alamar tambaya kan ko akwai yiwuwar juyin mulki, idan aka fiskanci kalubale nan gaba"

"Yanayin gwamnatin rikon kwaryar da suke son yi, zai yi kama da na fararen hula ne, suna da niyyar hada kai da wasu shugabannin siyasa, da wasu fararen hula domin ya yi kama da na fararen hula, amma kuma na soji ne".

Shirye-shirye dai sun kankama dan gudanar da zaben ranar 28 ga wannan watan na Maris idan Allah ya kai mu.

Sauti da bidiyo akan labarin