Tsokacin Ostreliya kan sakamakon binciken jirgin MH17 | Labarai | DW | 14.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsokacin Ostreliya kan sakamakon binciken jirgin MH17

Bayan sakamakon biciken da aka bayar na ranar Talata kan faduwar jirgin kanfanin kasar Malesiya a gabashin Ukraine, hukumomin kasar Ostreliya sun sanar da matsayinsu.

Tony Abbott Firaministan Ostareliya

Tony Abbott Firaministan Ostareliya

A wannan Laraba ce dai hukumomin kasar ta Ostreliya suka ce ba za su amince da duk wani ban tsoro ba, a daidai lokacin da suke neman hakkoki mutanansu daga shari'a. Daga cikin Fasinjojin jirgin 298 da suka rasu yayin wannan hadari dai, 38 dukanninsu 'yan kasar ta Ostreliya ne ko kuma suna zama a kasar. Duk dai da cewa sakamakon bai nuna wanda ke da alhakin kakkabo jirgin ba, amma kuma hukumomin kasar Ukraine da ma kasashen yamma, na zargin 'yan tawayan gabashin kasar ta Ukraine masu goyon bayan Rasha da aikata wannan laifi, zargin da tuni Rasha ta yi watsi da shi, inda ta dora alhakin hakan ga hukumomin Ukraine.