Tsohon sojin Ruwanda ya ɗaukaka ƙara | Labarai | DW | 18.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon sojin Ruwanda ya ɗaukaka ƙara

Tsohon sojin Ruwandan nan da ake zargi da hannu a kissan kiyashin 1994 ya ɗaukaka ƙarar hukuncin ɗaurin shekaru 25 da wata Kotu a Faransa ta yanke masa

Pascal Simnikangwa sojan Ruwanda nan na farkon da aka taɓa yi wa shari'a a Faransa bisa rawar da ya taka lokacin kisan kiyashin da aka yi a ƙasar a shekarar 1994, ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin ɗauri a gidan kasso na shekaru 25 da aka yanke masa.

Tsohon kaftin na sojin mai shekaru 54 na haihuwa ya sami wannan hukuncin ne bayan da aka shafe makonni shidda ana shari'a, wanda ya ɗauki hankalin Faransawa domin zargin sakacin da aka yi musu a wancan lokacin, inda mutane dubu 800 suka hallaka.

Lokacin shari'ar wanda aka fara gabannin bukuwan cika shekaru 20 da afkuwar kissan kiyashin, Lauyoyin sun ƙaryata duk shaidun da masu shigar da ƙarar suka gabatar suka kuma yi zargin cewa shari'ar ne bisa dalilai na siyasa.

Masu shigar da ƙarar na zargin Pascal, wanda ke amfani da kujerar guragu bayan hatsarin motar da yayi a shekarar 1986 da shirya kissar gillar da aka yi wa jamaa da kuma taimakwa makissan.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal