1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban ƙasar Iraqi Saddam Hussein ya yi kira ga `yan ƙasarsa da su fi mai da hankalinsu wajen fatattakar dakarun Amirka daga ƙasar.

October 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bufl

Toshon shugaban ƙasar Iraqi, Saddam Hussein, ya faɗa wa ’yan ƙasarsa cewa lokacin ’yantad da ƙasar ya kusanto. A cikin wata takardar da ya rubuta ta kan lauyoyinsa, Saddam ya yi kira ga duk ’yan Iraqin da su daina yaƙan juna saboda dalilan addini ko ƙabilanci, su fi mai da hankalinsu wajen ganin cewa sun cim ma nasarar fatattakar dakarun Amirka daga ƙasar. Babban lauyan tsohon shugaban, Khalil al-Dulaimi, ya ce Saddam da kansa ne ya sa shi rubuta takardar cikin larabci, wanda kuma ya rattaba hannunsa a kai tamkar babban kwamandan mayaƙan jihadi na rundunar sojin ƙasar. Hakan dai ya wakana ne a wata ganawar da ya yi da Saddam ɗin a ran asabar da ta wuce, a wani gidan yarin Bagadazan, inda yake tsare a halin yanzu. Babban Lauya al-Dulaimi ya ƙara da cewa sun shafe fiye da awa 4 suna tattaunawa tare da sauran lauyoyin da ke kare Saddam, a cikinsu kuwa har da tsohon antoni-janar na Amirka, Ramsey Clark.