1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon ministan kudin Madagascar ya lashe zaben shugaban kasar

January 3, 2014

Kotu a kasar Madagascar za ta bayyana wanda ya lashe zabe a zabukan shugaban kasar da aka gudanar biyo bayan zargin magudi da dan takarar jam'iyyar adawa ya yi.

https://p.dw.com/p/1Al4e
Madagaskar Wahlen Hery Rajaonarimampianina 20.12.2013
Hoto: Reuters

Sakamakon farko dai na kuri'un da aka kada a kasar ta Madagascar na nuni da cewa tsohon ministan kudin Hery Rajaonarimampianina ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a karon farko tun bayan juyin mulki na shekara ta 2009.

Hukumar zaben kasar ce ta bayyana Rajaonarimampianina, da ke samun goyon bayan shugaban kasar mai barin gado Andry Rajoelina da ya dane kan karagar mulkin bayan da aka kifar da gwamnatin Marc Ravalomanana da cewa shine ke kan gaba a kuri'un da aka rigaya aka kidaya.

Rajaonarimampianina dai ya lashe zaben da sama da kaso 53. na kuri'un da aka kada yayin da abokin takararsa Jean Louis Robinson, da yake samun goyon bayan tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana ya samu sama da kaso 46 kawai.

Mafiya yawan 'yan kasar dai na fatan cewa zaben da aka gudanar zai kawo karshen takunkumin karya tattalin arziki da duniya ta kakabawa Madagascar tun bayan kifar da gwamnatin Marc Ravalomanana a shekara ta 2009.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal