1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon ministan Jamus Klaus Kinkel ya rasu

March 5, 2019

Gwarzon dan siyasar Jamus kuma tsohon ministan harkokin wajen kasar Klaus Kinkel ya rasu yana da shekaru 82 a duniya

https://p.dw.com/p/3EU6W
Klaus Kinkel Politiker
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Balk

Kafin rasuwarsa Klaus Kinkel ya rike mukamai da dama inda ya zama babban jakadan Jamus daga shekarar 1992 zuwa 1998 ya kuma kasance shugaban jam'iyyar FDP mai rajin cigaban kasuwanci a tsakanin 1993 zuwa 1995

Shi ne kuma jami'in farar hula na farko da ya shugabancin hukumar leken asiri ta Jamus BND kafin daga bisani ya koma ma'aikatar shari'a inda ya zauna kusan shekaru goma.

Shugaban jam'Iyyar FDP Christian Linder ya baiyana Kinkel da cewa mutum ne jajirtacce mai karimci da kuma kwarjini.

A sakon ta na ta'aziyya shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nuna juyayi dangane da rasuwar gwarzon dan siyasar Klaus Kinkel wanda ta baiyana a matsayin abokin tafiya tun lokacin hadewar kasar Jamus.