Tsohon fraministan Kroshiya na fuskantar tuhuma | Labarai | DW | 20.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon fraministan Kroshiya na fuskantar tuhuma

Wata kotu a ƙasar ta yanke Ivo Sanader hukumcin ɗaurin shekaru goma na zaman gidan yari saboda zargin cin hanci da karɓar rashawa

Ivo sanader ɗan shekaru 59 da haifuwa wanda ya jagoranci gwamnatin yan kwansavati har so biyu tun daga shekarun 2003 zuwa 2009 .

Kotun ta tuhume shi ne da laifin karɓar wasu kuɗaɗen toshiyar baki har kusan euro dubu 480; daga wani kamfanin na ƙasar Hangari, wato Mol don sanyen hannayan jari kamfanin man fetur na Kroshiya ba bisa ƙaida ba.Ƙungiyar Tarrayar Turai dai na saka ido ,akan shara'a ta Sanader wanda ya yi fafutukar ganin ƙasar ta Kroshiya ta samu shiga a cikin ƙungiyar EU a shekara ta 2013.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi