Tsohon firaministan Tanzaniya ya fice daga jam′iyya mai mulki | Labarai | DW | 28.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon firaministan Tanzaniya ya fice daga jam'iyya mai mulki

A karon farko an samu jigo daga jam'iyya mai mulkin kasar Tanzaniya ya koma bangaren 'yan adawa, saboda abin da ya kira kama-karya.

Tsohon Firaministan Tanzaniya Edward Lowassa ya fice daga jam'iyya mai mulki ta Chama Cha Mapinduzi inda ya koma bangaren 'yan adawa, saboda abin da ya kira kama-karya na shugabanci, watanni uku kafin zaben kasa baki daya na kasar a ranar 25 ga watan Oktoba mai zuwa.

Lowassa dan shekaru 61 wanda ya rike makamun firaminista daga shekara ta 2005 zuwa 2008 ya bayyana komawa jam'iyyar adawa ta Chadema. Jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi ta tsayar da John Magufuli wanda minista ne a gwamnatin kasar a matsayin dan takaran shugaban kasa a zaben da ke tafe, inda Lowassa da sauran 'yan takara suka rasa. Jam'iyyar tana mulkin kasar ta Tanzaniya tun bayan samun mulki a shekarar 1964. Shugaba Jakaya Kikwete baya neman sake takara saboda ya kammala wa'adinsa na shekaru biyar sau biyu.