1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atal Bihari Vajpayee tsohon firaministan Indiya ya rasu

Salissou Boukari
August 16, 2018

Allah ya yi wa tsohon firaministan kasar Indiya Atal Bihari Vajpayee, rasuwa bayan da ya yi fama da wata doguwar rashin lafiya a birnin New Delhi.

https://p.dw.com/p/33GhT
Atal Bihari Vajpayee
Tsohon firaministan Indiya marigayi Atal Bihari VajpayeeHoto: Getty Images/AFP/P. Singh

A dazu-dazun nan ne aka sanar da rasuwar tsohon firaministan kasar Indiya Atal Bihari Vajpayee, mai shekar 93 da haihuwa, bayan da ya shiga cikin wani mawuyacin hali na rashin lafiya a birnin New Delhi. Firaminisrtan kasar ta Indiya ne dai na yanzu Narendra Modi, ya sanar da labarin mutuwar.

Vijapayee, ya jagorancin kasar ta Indiya ne har sau uku inda na farko a shekara ta 1996, sai na biyu a tsakanin shekara ta 1998 zuwa 1999 sannan wa'adi na uku ya yi shi ne daga shekara ta 1999 zuwa 2004.

Marigayin ya jima yana fama da rashin lafiya a cewar likitocinsa inda watanni biyu da suka gabata ma an kwantar da shi bayan da ya yi fama da matsalar koda da kuma jiyon kirji.