Tsohon firaiministan Izira′ila ya rasu | Labarai | DW | 11.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon firaiministan Izira'ila ya rasu

Ana ci gaba da mika sakon ta'aziya na rasuwar tsohon Firaministan Ariel Sharon Izira'ila

Kasashen duniya na ci gaba da mika sakon ta'aziyar rasuwar tsohon Firaministan Izira'ila Ariel Sharon, wanda ya shafe shekaru takwas cikin doguwar suma, kafin ya bar duniya a wannan Asabar (11. 01. 14) yana da shekaru 85 da haihuwa.

Tun cikin shekara ta 2006, Marigayi Sharon ya gamu da bugun jini, sannan ya sume.

Shugaban Amirka Barack Obama ya ce Marigayi Sharon ya mika rayuwarsa wa Izira'ila. Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce Sharon ya kasance jigo a cikin tarihin Izira'ila. Yayin da babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon kuwa ya ce marigayin gwarzo ne na Izira'ila.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh