Tsibirin Sardiniya na Italiya ya gamu da ambaliya | Labarai | DW | 19.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsibirin Sardiniya na Italiya ya gamu da ambaliya

An tabbatar da mutuwar mutane 18 sakamakon ambaliyar ruwa sama a Italiya

Ambaliyar ruwan saman da aka samu a tsibirin Sardiniya na ƙasar Italiya ta yi sanadiyar hallaka mutane 18, tare da rusa gidaje, da gadoji da awun gaba da motoci. Ambaliyar ta raba ɗarurruwan mutane na gidajensu.Wata guguwa mai ƙarfi ɗauke da ruwan sama ta haifar da wannan ambaliyar ruwan.

Hukumomin ƙasar sun kafa dokar ta ɓaci a tsibirin sakamakon faruwar lamarin, akwai mutane masu yawa da suka ɓace bayan faruwar ambaliyar ruwan. Firamnistan ƙasar ta Italiya Enrico Letta, ya kira taron gaggawa na majalisar zartas wa inda aka amince da kafa dokar ta bacin, domin ƙarfafa ayyukan ceto.

Mawallfi: Suleiman babayo
Edita: Abdourahamane Hassane