1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsibirin Guam zai kare kansa daga hari

Gazali Abdou Tasawa
August 10, 2017

Gwamnan tsibirin Guam da ke zama sansanin sojin Amirka a yankin Pacific ya bayyana cewa tsibirin ya dauki matakan iya tunkarar duk wani hari da zai fuskanta daga Koriya ta Arewa.

https://p.dw.com/p/2i1CO
USA Guam Gouverneur Eddie Calvo
Hoto: Imago/Kyodo News

Gwamnan tsibirin Guam da ke zama wani sansanin sojin Amirka a yankin Pacific ya bayyana a wannan Alhamis cewa tsibirin ya dauki matakan iya tunkarar duk wani hari da zai fuskanta daga Koriya ta Arewa wacce a jiya Laraba ta bayyana aniyar harar tsibirin da makamai masu linzami. 

Eddie Calvo Gwamnan tsibirin na Guam mai kunshe da mutane dubu 162 ya ce sun saba da jin irin wannan barazana daga Koriya ta Arewa tun bayan da Amirka ta girke sojojinta dubu shida a tsibirin na Guam, amma yana da kwarin gwiwar cewa Amirka ta dauki matakan kare tsibirin daga harin Koriya ta Arewa ko da hakan zai tabbata. Wata wadda ke da zama a tsibirin na Guam na daga cikin masu irin wannan tunani:

" Ni ban damu ba sosai ko da yake akwai wadanda suka razana matuka, amma ni ban ga dalilin damuwa ba domin na yi imanin Amirka za ta kare mu"

Ko a wannan Alhamis ma dai Koriya ta Arewa ta jaddada aniyarta ta harar tsibirin na Guam tare ma da bayar da karin haske kan shirin nata inda ta ce makamai masu linzami guda hudu da za ta harba zuwa tsibirin na Guam za su bi ta sararain samaniyar kasar Japan ne