Tsayar da Shawara da Kanka – Tsarin Iyali | Learning by Ear | DW | 17.02.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Tsayar da Shawara da Kanka – Tsarin Iyali

Tsarin Iyali

Tsarin Iyali

Al'umar Afirka na daɗa bunƙasa cikin hamzari. Amma a ɗaya hannun yawan albarkatu sai ƙara raguwa yake yi lamarin da ba shakka zai haifar da sabbin matsaloli. A cikin shirin muna ɗauke da bayani a game da matakan da mutum zai iya ɗauka don tsara iyalinsa.

Babban dalilin bunƙasar al'uma a cikin hamzari shi ne rashin matakai na wayar da kan jama'a. A cikin wannan salsalar zamu kawo muku bayanai akan matakan kariya, ba ma kawai game da ɗaukar ciki ba, har ma da cututtuka irinsu HIV/AIDS da sauran cuttukan da akan kamu da su ta hanyar jima'i. Hakazalika shirin zai kawo muku cikakkun bayanai a game da matakan tsara iyali.

Desire mai shekaru 16 da haifuwa ita ce jigon sabon shirin na rediyo. Bayan mutuwar mahaifiyarta ta shiga gwagwarmayar ɗaukar nauyin tarbiyyar yara biyar a yayinda a lokaci guda take ƙoƙarin neman ilimi. A daura da haka ya zama wajibi akan Desire ta kyautata dangantakarta da kakarta mai ra'ayin mazan-jiya dangane da rawar mace tsakanin dangi.

Al'amura sun ƙara yin tsamari bayan da matashiyar ta haɗu da Eiric mai shekaru 18 da haifuwa, wanda ba kawai abota yake so daga gare ta ba. Daga baya Desire ta gano wani muhimmin asirin babbar ƙawarta Lorraine….

Sauti da bidiyo akan labarin